SCAM-HUNTING TOOLS: Muhimman Kayan Aiki 15 Da Za Su Taimaka Maka Gano Online Scams
Bincika • Tabbatar • Kare Kanka A yau, online scams suna ƙara yawaita a WhatsApp, Telegram, Facebook, Email da sauran social media platforms. Scammers suna amfani da fake links, phishing websites, stolen images, fake accounts da kuma sunayen manyan companies domin yaudarar mutane. Amma ba sai ka kasance cybersecurity expert ba kafin ka fara binciken suspicious message ko link. Akwai wasu free online tools da za su iya taimaka maka wajen tattara information da gano wasu red flags . A wannan post ɗin, zan bayyana wasu daga cikin muhimman Scam-Hunting Tools , abin da kowannensu yake yi, da kuma misalin lokacin da zaka iya amfani da shi. 1. VirusTotal.com VirusTotal yana taimaka maka wajen binciken suspicious links, files da wasu domains. Yana haɗa sakamakon security engines daban-daban domin nuna ko an taɓa gano wani threat. Example: Idan wani ya turo maka wani strange link kamar example-giveaway.com , zaka iya saka URL ɗin a VirusTotal kafin ka buɗe shi. 2. WH...