HATSARIN AMFANI DA PUBLIC WI-FI: ABUBUWAN DA YA KAMATA KA SANI KAFIN KA SHIGA ACCOUNT ƊINKA
A wannan zamanin na Digital Technology , mutane da yawa suna amfani da Wi-Fi na jama'a domin shiga internet cikin sauƙi. Ana iya samun Public Wi-Fi a hotels, restaurants, airports, schools, shopping centres da wasu wuraren jama'a. Amma abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne cewa wasu Public Wi-Fi networks na iya zama haɗari ga privacy da online security ɗinka. Idan ba ka yi taka-tsantsan ba, wasu bayananka na iya shiga hannun mutane marasa kyau. 💡 MENENE PUBLIC WI-FI? Public Wi-Fi wata hanyar internet ce da mutane da yawa za su iya amfani da ita a wuraren jama'a. Wasu suna buƙatar password, yayin da wasu kuma kowa zai iya shiga kai tsaye. Misali, kana zaune a restaurant sai ka ga network mai suna "Free Wi-Fi" . Ka haɗa wayarka domin browsing ko amfani da social media. Wannan shi ake kira amfani da Public Wi-Fi. MUHIMMIN DARASI Ba duk Wi-Fi da aka rubuta "Free" ko "Public" ba ne yake da cikakken tsaro. Wasu networks ...