YADDA AKE GANE FAKE LINK KAFIN KA DANNA SHI
YADDA AKE GANE FAKE LINK KAFIN KA DANNA SHI A wannan zamanin na Digital World , links suna da matuƙar amfani wajen kai mu zuwa websites, social media pages, online forms da sauran bayanai. Amma ba kowanne link da ka gani bane yake da aminci. Wasu masu damfara suna amfani da fake links domin su yaudari mutane, su kai su zuwa websites na bogi, ko kuma su nemi su shigar da bayanansu na sirri. MUHIMMIN DARASI KADA KA DANNA KOWANNE LINK BA TARE DA KA DUBA SHI BA Kafin ka danna wani link, ka ɗauki lokaci ka tabbatar da inda zai kai ka. Ɗan ƙaramin bincike na iya taimaka maka wajen kare account ɗinka da bayananka. 1. KA DUBA SUNAN WEBSITE DA KYAU Masu damfara suna iya ƙirƙirar link mai kama da na official website. Suna iya canza harafi guda ko ƙara wata kalma domin link ɗin ya yi kama da na gaskiya. Ka duba spelling na sunan website sosai kafin ka danna ko ka shigar da wani bayani. 2. KA YI TAKATSANTSAN DA LINKS DA AKA TURO MAKA BA TARE DA KA NEMA BA Id...